Thursday, 16 June 2016
Sheikh Ja'afar Mahmud Adam - Babu Tilastatwa ga Shiga Addini
Yan uwa musulmi, ya kamata muyi iya kokarin mu wurin wayar ma da mabiya wasu addinan kai cewa ayyuka irin na Boko Haram da IS (wato Islamic State) ko kusa basuyi da koyarwar addinin musulunci ba.
Wannan hakki ne da ya rataya akan mu a matsayin mu na musulmi.
Malaman mu sun yi iya nasu aikin wurin yi muna bayani daga tanade tanaden Alqur'ani da sunnah.
Saboda haka sauran aikin ya rage namu na muyi ta kokari wurin yadawa, har sai wadanda ba musulmi ba sun fahimta.
Allah Ya bamu ikon daurewa akan yima addini aiki, Ya amfanar damu abinda muka ji Ya kuma bamu ikon yin aiki da shi.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment